Boko Haram: An bude makarantu a Gwoza

Sojojin Nigeria a bakin aiki Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Sojojin Nigeria na kokarin cika wa'adin watanni uku da shugaba Muhammadu Buhari ya ba su na su kawo karshen tada kayar bayan mayakan na BH.

Rahotanni daga garin Gwoza da ke arewacin jihar Borno na cewa al'amura sun fara komawa daidai, bayan da 'yan gudun hijira suka fara komawa gidajensu.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da dakarun sojin kasar suka fatattaki mayakan BH tare da lalata sansanonin da suka kafa a garin na Gwoza, kuma tuni aka bude makarantun Firamare da ke garin inda dalibai suka koma karatu.

Mai magana da yawun rundunar Sojin kasar Kanar Sani Usman Kuka-sheka ya tabbatarwa BBC cewa an hade makarantun Firamare da ke garin ta hanyar tattare daliban a makaranta guda dan su ci gaba da daukar karatu.

Shi ma wani mazaunin birnin Maiduguri da ya kai ziyarar gani da idonsa garin na Gwoza yace lamurra sun fara komawa daidai, mutane na kokarin dawo da al'umaran da suke gudanarwa na yau da kullum a garin.

To sai dai kuma ya koka da cewa har yanzu mayakan na BH su na tare su a hanya matukar ba sa tare da rakiyar dakarun sojin da ke kula da wannan yankin, idan sun fito daga garin na Gwoza za su je sayayyar kayan bukatu ko ziyara wasu garuruwa makofta.

A dan haka sun bukaci da a kafa musu shingayen bincike na jami'an tsaro a kan hanyoyi, dan kare su daga mayakan na BH.