An kashe jami'in 'yan sanda a yankin Sinai

'Yan sandan Masar Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ba wannan ne karo na farko da 'yan IS suke harbe jami'an tsaro a kasar Masar ba.

Wasu 'yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun harbe har lahira wani babban jami'in 'yan sanda a arewacin yankin Sinai na kasar Masar.

Wannan shi ne karo na biyu cikin kwanakin nan da ake harbe jami'in 'yan sanda,ma'aikatar cikin gida ta kasar ta ce an harbi Birgediya Janal Ahmed Abdel Satar a wajen caji ofis din 'yan sanda da ke babban birnin yankin Al-Arish.

A farkon wannan watan ne jami'an tsaro suka fara kaddamar da hare-hare akan mayakan jihadi na kungiyar IS da ke yankin Sinai.

Masu ikirarin kafa daular musuluncin dai sun kashe daruruwan jami'an 'yan sanda da sojoji tun bayan da aka fara juyin juya hali a kasar ta Masar shekaru biyu da suka gabata.