Sojoji sun yi wa Ouagadougou tsinke

Image caption Jagoran sojojin da suka yi juyin mulki

Manyan hafsoshin sojin Burkina Faso sun bukaci dakarun da suka jagoranci juyin mulki a makon da ya gabata su mika makamansu.

A cewarsu, dakarun sojin kasar za su yi maci zuwa Ouagadougou babban birnin kasar domin cimma wannan bukatar.

"Duka sojojin kasar za su taru a Ouagadougou domin kwace makaman dakarun fadar shugaban kasa ba tare da an zubar da jini ba," in ji wata sanarwa

Galibin wadanda suka yi juyin mulkin, sojoji ne na hannun damar tsohon shugaban kasar Blaise Compaore , wanda aka tilasta wa sauka daga mulki a bara.

A ranar Alhamis ne sojoji suka kifar da shugaban kasar mai rikon kwarya Michel Kafando daga kan kujerarsa.

Manyan hafsoshin taron sun bukaci sojojin da suka yi juyin mulkin da su mika makamansu domin su tsira da mutuncinsu.