Menene makasudin juyin mulkin Burkina Faso?

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Laftanal-Kanar Mamadou Bamba kenan, wanda ya sanar da juyin mulkin a gidan talabijan din kasar, ranar Alhamis.

Wakilin BBC Lamine Konkobo ya duba al'amarin da ya janyo sojojin kasar Burkina Faso suka yi juyin mulki ana shirin zaben shugaban kasar da zai maye gurbin wanda aka hambarar a bara, Blaise Compaore da ya dade yana mulkin kasar, a wata mai zuwa.

'Dalilin juyin mulki'

Dakarun da ke gadin fadar shugaban kasa, watau (RSP), wanda tsohon shugaban kasar Blaise Compaore ya kaddamar, sun ce ba su ji dadin yadda a bara sabuwar dokar zaben kasar ta hana wadanda suka nuna ra'ayin shiga takarar shugaban kasa a shekarar da ta gabata ba, kuma wannan yunkurin ne ya hambarar da gwamnatinsa a watan Okbobar shekarar 2014.

Amma menene asalin matsalar dakarun? Sojojin sun damu ne da cewar sabuwar gwamnati za ta iya soke rundunar ta su.

Menene matsayin masu gadin fadar shugaban kasa?

Masu gadin fadar shugaban kasa sun hada ne da manya masu fada a ji su kusan 1,300 da ke goyon bayan Mista Compaore, ya kuma kaddamar da su ne gabannin kisan da aka yi wa tsohon shugaban da ya maye gurbinsa, kuma abokinsa Thomas Sankara, lokacin da aka yi juyin mulkin da ya daure Mista Compaore kan karagar mulki.

Dakarun da ke gadin fadar shugaban kasar suna da kayan aiki da kuma horo ta musamman, abin da ya sa wasu lokuta suke yin gaban kan su, ba tare da neman shawarar rundunar sojin kasar ba.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Zanga-zanga ta barke a Wagadugu Babban birnin kasar, bayan an kama shugaban kasa mai rikon kwarya, da Firayi Ministan kasar, ranar Laraba.

Mutanen kasar na tausayawa dakarun RSP kuwa?

Yawancin mutanen da suka goyi bayan hambarar da gwamnatin Compaore sun kosa a tarwatsa dakarun RSP, amma an fi zaton mambobin tsohuwar jam'iyyar da ke mulki CDP tana murna da wannan lamari, saboda dama sun yi zaton an hana su shiga takarar zabukan ne saboda alakar su da tsohon shugaban kasar.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Blaise Compaore ya yi mulkin kasar Burkina Faso, tun daga shekarar 1987 har shekara 2014.

Tsohon shugaban kasar yana fada a ji kuwa a Burkina Faso?

Wasu na tunanin cewa Mista Compaore, wanda yanzu haka ke neman mafaka a kasar Ivory Coast, yana da hannu a wannan juyin mulki, a yunkurinsa na neman dawowa kan mulkin kasar.

Shugaban kasar Ivory Coast Alassane Ouattara ya samu goyon baya wurin Mista Compare lokacin yakin neman zabe a kasarsa domin haka ake tunanin shi ma bai ji dadin yadda lamarin ya kaya ba.

Yaya rayuwar mutanen kasar Burkina Faso?

Burkina Faso na cikin kasashen da ke fama da talauci, kuma mutanen garin na cikin matsanancin halin rashi, inda matasa ke fama da rashin aiki sanadiyyar cin-hanci da rashawa da ya yi wa kasar katutu.

Mutanen garin sun sa ran cewar, canjin hannun mulki da dimokradiyya ta kawo za ta kawo ingantacciyar canji ga rayuwar kasar, saboda haka ne suke wa juyin mulkin da aka yi kallon koma baya ne a garesu.

Abubuwa bakwai da ba ka sani ba a kan Burkina Faso

Hakkin mallakar hoto AFP

*** Tana cikin kasashen da suka fi talauci a duniya, duk da suna kasuwancin fitar da auduga.

*** Kasar Faransa ce ta raine su, kuma sun 'yanta su a shekarar 1960, da sunan Upper Volta.

*** Kyeftin Thomas Sankara wanda aka fi sani da 'Africa's Che Guevara' ya kwace mulkin kasara a shekara 1983 inda ya sauya kundin tsarin mulkin kasar.

*** Thomas Sankara ya canza wa kasar suna zuwa Burkina Faso, wanda ke nufin 'kasar mai gaskiya'

*** Mista Compaore ya na da hannu a juyin mulkin da ya kashe Mista Sankara, kuma ya yi mulki har shekaru 27, kafin a hambarar da shi a bara.

*** Ana kiran mutanen Burkina Faso da 'Burkinabes' kuma suna da sha'awar tukin babur.

*** An san su da wani fitaccen biki mai suna Fespaco, da ake yi duk bayan shekaru biyu a Wagadugu babban birnin kasar.

Yaya wannan sabon lamari zai shafi sauran yankin?

Ana sa ido ko da lamarin zai sa fitina ta barke, domin idan rundunar sojin kasar suka sa baki kuma dakarun da ke gadin fadar shugaban kasar suka ki mika mulki, toh lamarin zai baci.

An damu da cewar bacin lamarin zai kai ga shigowar masu ikirarin kafa daular Musulunci da ke aika-aika a kasar Mali da sauran kasahen yankin, an kuma san za su yi saurin amfani da wannan dama domin samun wurin zama a arewacin Burkina Faso.