Kauyen Misra da ake yawan tura yara ci-rani

Image caption Kauyen Aghour al-Sughra suna cikin kauyuka da dama a Misra da ke yawan tura yara ci-rani Turai.

A ci gaba da fama da matsalar 'yan gudun hijira da kasashen Turai ke yi, har yanzu masu zaman makokin iyalan su na neman dalilan ibtila'in da ba a taba samu irin sa a Misra, a cikin 'yan shekarun nan.

Mutane biyu da suka rayu sun bayar da shaidar cewa sama da mutane 500 ne suka mutu kuma mutane 11 kacal suka rayu, sakamakon jirgin ruwan masu fasa kaurin da ya kade nasu wanda ya fito daga garin Damietta a Misra kusa da kasar Malta, kuma jirgin ya nutse bayan hakan.

Yawancin fasinjojin jirgin sun fito ne daga Syria da Gaza, amma mafi yawanci 'yan kasar Misra ne wadanda suka hada da yara kanana, kuma wasu su 12 cikin yaran da suke bace, sun fito ne daga wani kauye da ke wajen birnin Alkahira.

Iyalan wadanda ake nema sun gudanar da sabon kara a gaban kotun Misra, domin neman gwamnati ta dauki alhakin iyalan su da suka rasa.

Image caption Ana ceto 'yan ci-rani da suka nutse a tekun Bahar Rum a kokarin su na tsallakawa zuwa Turai.

'Daukaka Kara'

Wannan shi ne karo na uku da suke shigar da kara, saboda har yanzu suna kyautata zaton wadansu daga cikin iyalan nasu na nan da ransu a tsare hannun jami'an tsaron Misra.

Wani kauye mai suna Aghour al- Sughra da aka san su dama da tura yara ci-rani Turai, sun tura 'yan kauyen kusan 3,000 garin Turin da ke arewacin Italiya.

Dan kauyen Aghour al-Sughra mai suna Essam Ahmed, mahaifin wani yaro Mohammed da ya ke cikin jirgin da ya nutse, shi ma ya neman gwamnatin kasar ta yi masa adalci.

Kauyukan Misra suna zama ne cikin tsatsan talauci, dalilin haka yaran ke kokarin barin kasar, suna cewa babu alamun za su samu ingantacciyar rayuwa ga duk sabbin gwamnatocin kasar.

Wani da suke kira 'Mandoob' ne ke yi masu hanyar tsallaka tekun, inda yake samun nasa rabon a kudin jirgin da suke biya, amma bana shi ne jagoran iyalai wurin neman yaran nan su 12 da suka bata.

Kauyen Aghour al-Sughra ana daya daga cikin kauyuka da yawa a Misra da ke da yawan masu fita ci-rani, kuma Salama Abdel Karin ya dawo daga Turin bayan shekaru 23 yana kuma gina wa iyalan sa wani kasaitaccen gida a wajen Aghour al-Sughra.

Ya ce, "duk yaran da suka samu tafiya cirani sun dawo sun taimakawa kauyen wurin kasuwanci, duk abinda ka gani a kauyen nan akwai hannun mu a ciki".