'Musulunci bai dace da tsarin Amurka ba'

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ben Carson yana takarar shugabancin Amurka

Dan takarar shugabancin Amurka na jam'iyyar Republican, Ben Carson ya ce addinin Musulunci bai dace da kundin tsarin mulkin kasar ba.

Ben Carson -- wanda tsohon likitan kwakwalwa ne -- ya ce ba zai taba lamintar kasancewar musulmi a matsayin shugaban Amurka ba.

Kalaman nasa na zuwa ne 'yan kwanaki bayan babban dan takarar shugabancin kasar a karkashin jam'iyyar ta Republican, Donald Trump, ya ki yarda ya nesanta kansa daga wani mai goyon bayansa da ya soki shugaba Obama da cewa Musulmi ne kuma ba dan Amurka ba ne.

Da yake mayar da martani, James Zogby, shugaban cibiyar Larabawa 'yan Amuka, ya shaida wa BBC cewa ra'ayin da Mista Carson ya bayyana wani abu ne na rashin hankali.