Malamai na yajin aiki a Kenya

Hakkin mallakar hoto others
Image caption Malaman sun ce gwamnati ba ta biyan su albashi yadda ya kamata.

An rufe dukkan makarantun gwamnati a kasar Kenya sakamakon yajin aikin makonni uku da malamai suka fara ranar Litinin domin matsa lamba kan gwamnati ta kara musu albashi.

Kotun Kolin kasar ce dai ta bai wa gwamnatin umarnin biyan karin kashi 50 na albashin ga malaman, sai dai gwamnatin na kalubalantar batun.

Shugaba Uhuru Kenyatta ya ce ana biyan malaman albashin da ke isar su, yana mai cewa karin albashin zai kawo matsala a harkokin kudin gwamnati.

Malaman sun sha cewa gwamnati ta sanya hannu a yarjejeniyar karin albashin tun a shekarar 1997, kuma har yanzy ba ta ba su albashin yadda ya kamata.

Sai dai Shugaba Kenyatta ya musanta hakan, yana mai cewa gwamnati na biyan malaman ciakken albashi.