An yi garkuwa da Cif Olu Falae

Rahotanni daga Nigeria na cewa an sace tsohon sakataren gwamnatin tarayyar kasar, Cif Olu Falae a jihar Ondo da ke kudancin kasar.

Bayanai sun nuna cewar an yi awon gaba da shi ne a gidansa da ke Akure babban birnin jihar Ondo.

Falae mai shekaru 77 da haihuwa ya rike mukamin sakataren gwamnatin Nigeria ne a zamanin mulkin tsohon shugaban kasar Janar Ibrahim Badamasi Babangida.

Cif Olu Falae jigo ne a kungiyar 'yan kabilar Yarabawa zalla mai sun Afenifere kuma ya yi takarar mataimakin shugaban kasa a shekarar 1999 a karkashin inuwar jam'iyyun hadaka na AD da APP tare da Alhaji Umaru Shinkafi.