Kamaru: An kashe 'yan Boko Haram 15

Hakkin mallakar hoto AFP

Rahotanni daga garin Amchide na jamhuriyar Kamaru dake kan iyaka da Najeriya na cewa, dakarun Kamaru sun kashe wasu mahara 15 da ake zaton 'yan Boko Haram ne, yayin wani artabu.

Sojojin sun kuma murkushe wani yunkurin harin kunar bakin wake a wayewar garin yau a garin Gouzoudou kusa da Mora.

Wannan dai shi ne harin kunar bakin wake na 11 da aka kai a lardin arewa mai nisan na Kamaru tun daga watan Yuli, wanda kuma suka yi sanadiyar mutuwar mutane 100.

Kamaru tana cikin kasashen da suka yi hadakar dakaru domin yaki da Boko Haram.