A shirye muke mu mika mulki - Diendere

Hakkin mallakar hoto
Image caption Janar Gilbert Diendere

Babban jami'in soja daya jagoranci juyin mulki a Burkina Faso ya shaidawa BBC cewa a a shirye yake ya mika mulki ga gwamnatin farar hula.

Sai dai Janar Gilbert Diendere wanda ya sanar da hakan ta wayar tarho daga wani sirrataccen wuri, ya ce zai yi hakan ne kadai idan har shugabannin kasashen Afirka ta yamma suka tabbatar da sharuddan dake kunshe a cikin yarjejeniyar da aka cimma a karshen mako.

Sharuddan sun hada da yafewa dakarun da suka yi juyin mulkin, da kuma gudanar da zabe a watan Nuwamba.

Sojojin kasar masu goyon bayan gwamnatin farar hular da aka hambarar sun isa wajen babban birnin kasar Wagadugu.

In anjima a yau ne shugabannin kasashen Afirka ta yamman zasu yi taro a Najeriya.