Kotu ta bayar da belin Bukola Saraki

Image caption 'Yan majalisar dattawa da dama ne suka raka Saraki kotun.

Shugaban kotun kula da da'ar ma'aikata ta Najeriya, Danladi Umar, ya bayar da belin shugaban Majalisar dattawan kasar, Bukola Saraki.

Saraki ya gurfana a gaban kotun ne bisa zarge-zarge goma sha uku -- cikin su har da zargin kin bayyana kadarorin da ya mallaka.

Shugaban Majalisar dattawan, wanda ya gurfana a kotun da safiyar ranar Talata, ya musanta zarge-zargen.

Shugaban kotun ya ce ya bayar da belin Saraki ne "a matsayin sa na dan Najeriya wanda ke rike da babban mukami", yana mai cewa zuwan sa kotun ya nuna cewa ba zai karya dokokinta ba ko da an bayar da belin sa.

Za a ci gaba da sauraren karar ranakun 21 da 22 da 23 ga watan Oktoba.

'Yan Majalisa sun yi masa rakiya

Saraki ya isa kotun da ke Abuja ne tare da rakiyar wasu 'yan majalisar dattawan kasar da tsohon shugaban jam'iyyar PDP, Abubakar Kawu Baraje.

A cikin 'yan majalisar dattawan da suka yi masa rakiya har da: mataimakinsa, Ike Ikweremadu da Aliyu Magatakarda Wamakko da Danjuma goje da Kabiru Gaya.

Kotun dai tana zargin sa ne da laifuka goma sha uku, wadanda ke da alaka da kin bayyana kadarorinsa yadda ya kamata a lokacin da yake gwamnan jihar Kwara.

Shugaban Majalisar dattawan ya kara da cewa zai je gaban kotun ne a matsayin na wanda yake biyayya ga dokokin kasar.

A baya dai Bukola Saraki ya ki gurfana a gaban kotun, yana mai cewa ba zai yi hakan ba saboda ya kai karar ta wata babbar kotun Abuja wacce ta bayar da umarni a dakatar da gurfanar da shi.

Kotun ta kula da da'ar ma'aikata dai ta bai wa Babban Sufeton 'yan sandan kasar ya kai mata Mr Saraki ranar Talata idan har ya ki mutunta umarninta.