Shugabannin ECOWAS na taro a Abuja

Image caption Ana saran taron zai warware rikicin Burkina Faso

Shugabannin kasashen kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ta ECOWAS ko kuma CEDEAO na wani taron koli na musamman, a Abuja, babban birnin Najeriya da zummar warware rikicin kasar Burkina Faso.

Tuni dai kungiyar ta tura wata tawagar masu shiga tsakani a karkashin jagorancin shugabannin kasashen Senegal da Benin zuwa kasar ta Burkina Faso, wadanda kuma suka sanar da fito da wani tsarin cimma sulhu.

Kasar Burkina Faso dai daya daga cikin kasashen kungiyar ta ECOWAS ko CEDEAO guda 15.

Shugabannin kasashen da ke taron sun hada mai masaukin baki Nigeria, da na Ghana, Senegal, Niger, Togo, Benin, Sierra Leone, Mali, Liberia, Ivory Coast da kuma Guinea.

Rikici a Burkina Faso dai ya janyo abubuwa sun tsaya cik a kasar inda shugabannin kasashen duniya suka bukaci sojoji su mai da mulki ga gwamnatin rikon kwarya karkashin jagorancin Michel Kafando.