An rusa dubban gidaje a kusa da Sinai

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sojojin Masar sun rusa kusan dukkanin gine-gine da ke nisan kilomita daya daga kan iyaka da Gaza.

Kungiyar kare hakkin bil adama ta 'Human rights watch' ta ce gwamnatin Masar ta rushe fiye da gidaje dubu uku da sauran gine-gine a yankin Sinai.

A cewarsu matakin ya saba wa dokokin kasa da kasa.

Sojoji sun soma ne da kona gidajen da ke kan iyaka da Gaza a shekarar 2013 domin a toshe duk wata hanyar shigowar mayakan sa kai da ke kawo hari.

Human rights watch ta zargi gwamnatin da rashin bai wa masu gidajen damar kintsi ko diyya bayan an rusa muhallansu, duk da cewar Masar ta musanta haka da cewa an yi rusau ne da yardar masu gidajen.

'Yan ta da kayar baya da ke zaune a arewacin Sinai da ke da alaka da masu ikirarin kafa daular musulunci watau IS, sun kara kaimi a hare-haren da suke kai wa tun da sojojin kasar suka hambarar da gwamnatin Shugaba Mohammed Morsi a watan Yulin shekarar 2013.

Tarzomar ta yi sanadiyyar hallaka mutane 3,600 wadanda suka hada da fararen hula da jami'an tsaro da suma masu ta'addancin.

Rahotanni da kungiyar ta tattaro sun yi nuni cewar kashi biyu cikin ukun lissafin kashe-kashen ya auku ne bayan gwamnati ta sanar da niyyar ta na rushe gidajen kan iyakar a watan Oktobar shekarar 2014.

'Kora dole'

Hotuna da bidiyo da aka samu daga tauraron dan Adam, da kuma tuntubar mazauna da wurin da kungiyar HRW ta yi, sun nuna cewa sojoji sun yi amfani da nakiyoyi da abubuwa fasa duste wajen rushe kusan duka gidaje da gonaki da ke da nisan kilomita daya daga kan iyakar Gaza.

Duk da gwamnati ta jaddada cewa manufar yin haka ita ce domin rufe duk wata hanya da ke baiwa masu tayar da kayar baya damar shigowa da makamai, ko ma wasu shawarwari da suke zargin suna samu daga kungiyoyin ta'addanci da ke garin Gaza kasar Falasdinu.

Kungiyar ta ce gwamnatin Masar da ta Isra'ila sun furta da kansu cewa, an fi samun shigowar makaman ta'addanci daga kasar Libya, ko ma daga hannun sojojin Masar.

Rahoton na HRW ya ce, wadannan matakai na korar jama'a daga muhallansu ya keta dokar kare hakkin bil adama ta Majalisar Dinkin Duniya da ta Kungiyar tarrayar Afrika wacce ita ma Masar ke ciki.

Gwamnatin Masar dai ta ce bata keta wani doka ba, kuma ta bi ka'idar da ke kula da hakkin bil adama ta kasa da kasa, wanda ke kula da rayuwar fararen hula da kuma kayayyakin su daga duk wani mummunar sauyin yanayi.