'Ban yi laifin komai ba'- Saraki

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Saraki ya ce zai gurfana a gaban kotun domin wanke kansa daga zargi.

Shugaban Majalisar dattawan Najeriya, Bukola Saraki, yana can a gaban kotun kula da da'ar ma'aikata domin wanke kansa daga zargin kin bayyana kadarorin da ya mallaka, kuma ya ce shi bai aikata laifin da kotun ke zargin sa da shi ba.

Saraki ya isa kotun da ke Abuja ne tare da rakiyar wasu 'yan majalisar dattawan kasar da tsohon shugaban jam'iyyar PDP, Abubakar Kawu Baraje.

A cikin 'yan majalisar dattawan da suka yi masa rakiya har da: mataimakinsa, Ike Ikweremadu da Aliyu Magatakarda Wamakko da Danjuma goje da Kabiru Gaya.

Kotun dai tana zargin sa ne da laifuka goma sha uku, wadanda ke da alaka da kin bayyana kadarorinsa yadda ya kamata a lokacin da yake gwamnan jihar Kwara.

Shugaban Majalisar dattawan ya kara da cewa zai je gaban kotun ne a matsayin na wanda yake biyayya ga dokokin kasar.

A baya dai Bukola Saraki ya ki gurfana a gaban kotun, yana mai cewa ba zai yi hakan ba saboda ya kai karar ta wata babbar kotun Abuja wacce ta bayar da umarni a dakatar da gurfanar da shi.

Kotun ta kula da da'ar ma'aikata dai ta bai wa Babban Sufeton 'yan sandan kasar ya kai mata Mr Saraki ranar Talata idan har ya ki mutunta umarninta.