Volkswagen ya shiga tsaka mai wuya

Hakkin mallakar hoto d
Image caption Hannun jarin Volkswagen ya yi kasa

Kamfanin kera motoci na kasar Jamus, Volkswagen ya ce ya ajiya sama da dala biliyan bakwai domin tunkarar rikicin gurbataccen hayakin da motocinsa ke fitarwa, matsalar da yanzu ta dabaibaye shi.

Kamfanin ya ce zai yi amfani da kudin ne wajan gano inda matsalar ta ke da kuma daukar matakan dawo da martabarsa a idanun kwastamominsu.

Kamfanin ya ce motocin da ke amfani da man dizel miliyan bakwai ne a duk fadin duniya aka sawa wata manhajar rage ainihin gurbataccen hayakin da mota ke fitarwa.

Birtaniya ta ce tana neman da a gudanar da bincike kan matsalar a duk fadin kasar.