Shugaba Abdrabbuh Hadi ya koma Yemen

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaban kasar Yemen, Abdrabbuh Mansour Hadi ya komo kasarsa bayan neman mafaka da aka tirsasa masa a watan Maris.

Shugaban kasar Yemen, Abdrabbuh Mansour Hadi ya koma birnin Aden da ke kudancin kasar, a karo na farko tun da aka tirsasa masa neman mafaka a Saudiyya.

Ana kyautata zaton zai kwana biyu a Aden kafin ya wuce zuwa taron da Majalisar Dinkin Duniya ke yi a birnin New York na Amurka.

Mista Hadi ya tsere ne daga Yemen a wata Maris, gabannin shigowar mayakan Houthi, kafin rundunar hadin gwiwar da Saudiyya ke jagoranta su kore su.

Masana sun ce dawowar Mista Hadi, wata alama mai muhimmanci, da ke nuna cewar gwamnatin Yemen ta soma dawo da martabarta a wani sashen kasar.

Kuma hakan na nufin akwai wani bangare da gwamnatin kasar ke iko da shi a Yemen din.