Za a kai naman hadaya Nigeria daga Makka

Image caption Masallacin Harami Makka

A karon farko, a bana za a kai naman hadayar dabbobin da aka yanka a kasar Saudia zuwa mabukata a arewa maso gabashin Nigeria.

Bankin Ja'iz wanda a bana zai fara yi wa mahajjatan Nigeria hadaya ya ce jihohi da dama a kasar sun ba shi aikin yin hadayar.

Bankin ya ce za a raba naman ga kasashen duniya mabukata, ciki har da Nigeria.

Malam Ismaila Adamu jami'in bankin ne na Ja'iz wanda ke jagorantar yanka dabbobin na hadaya a kasar Saudi Arabia, ya ce matsalar Boko Haram da aka samu a jihohin arewa maso gabashin Najeriya ce ta sa za a kai wa jihohin naman.

Ya ce da ma duk shekara ana kai naman hadaya daga Saudiya zuwa kasashen duniya da ke fama da matsaloli.