An bude babban masallacin Moscow

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Masallacin zai dauki mutane 10,000

An sake bude masallaci mafi girma a birnin Moscow, inda shugaba Putin da takwarorinsa na Turkiyya da Falasdinu suka halarci bikin.

Shekaru hudu da suka wuce ne, aka rusa masallacin domin a sake gina shi domin ya iya cin Musulmi masu ibada su 10,000.

Masallacin na daga cikin manyan masallatai uku a kasar Rasha, kamar irin wadanda ake da su a Chechnya da kuma Dagestan.

Mr Putin ya ce masallacin zai kasance cibiyar ibada da kuma ilimantar da mutane mabiya addinai daban-daban.

Ya jinjinawa shugabannin Musulmi a Rasha saboda nuna ba-sani ba-sabo ga masu tsatstsaurar ra'ayi.

An gina sabon Masallacin ne a inda tsohon yake wanda aka gina shi tun a shekarar 1904.

Wannan Masallacin na daga cikin Masallatai shida kacal da ake da su a Moscow duk da cewar akwai Musulmai kusan miliyan biyu a birnin.

Hakkin mallakar hoto AFP Getty
Image caption Shugaba Vladmir Putin da Recep Tayyip Erdogan na Turkiyya da kuma Mahmoud Abbas na Falasdinawa sun halarci bikin

Sannan kusan masu ibada 200,000 ne Sallah a kan titi lokacin bukukuwar Sallah.