An saki 'mai tsaron lafiyar' Osama Bin Laden

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption An saki Shalabi ne bayan ya kwashe shekara-da-shekaru a gidan yari.

Hukumar tsaron Amurka ta ce ta saki wani tsohon mai tsaron lafiyar shugaban Al- Qaeda, Osama Bin Laden daga gidan yarin Guantanamo Bay.

Yanzu dai an kai mutumin, Abdul Shalabi, mahaifarsa, wato kasar Saudiya.

Jami'an tsaron Pakistan ne suka kama Shalabi a shekarar 2001, sannan suka aika da shi gidan yarin na Amurka da ke kasar Cuba, inda ya yi yajin cin abinci saboda tsarewar da aka yi masa.

Sakin da aka yi masa na nufin yanzu akwai fursunoni 114 da ake ci gaba da tsarewa a Guantanamo, cikin su har da guda 52 wadanda aka amince a sauya musu gidan yari.

Wani kwamiti ne dai ya bukaci a saki Shalabi, ko da ya ke kwamitin ya ce akwai yiwuwar Shalabi ya ci gaba da goyon bayan 'yan ta'adda.

Yanzu dai za a yi kokarin sauya tunanin Shalabi a kasar Saudiyya.