Tarayyar turai za ta tallafa wa masu hijra

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Tarayyar turai za ta tallafa da Yuro biliyan daya

Shugabannin tarayyar turai da suke taron gaggawa a Brussels kan yadda za a magance matsalar masu kaura, sun amince da su samar da tsabar kudi har Yuro biliyan daya domin tallafawa 'yan gudun hijrar.

Sai dai kuma shugabannin sun ce za a tallafa wa masu hijrar ne wadanda suke a kasashe makwabtan Syria.

Da yake bayyana wannan kudiri, shugaban majalisar tarayyar turan, Donald Tusk ya ce za a sanya kudaden ne a asusun hukumomin majalisar dinkin duniya masu dawainiya da 'yan gudun hijra wadanda kuma suke aiki a kasar Lebanon da Jordan da kuma Turkiyya.

Ya ce yankin na turai ya dauki wannan mataki ne na tallafa wa 'yan hijrar domin tsayar da masu kaurar a cikin kasashen yankin larabawa.

Mista Tusk ya kara da cewa su kuma kasashen na turai za su ci gaba da tsare kan iyakokinsu.