'Ba sa so a kawar da Boko Haram'

Rundunar sojojin Najeriya ta bankado wasu mutane masu karfin fada-a-ji a arewa maso gabashin Najeriya da ke dakile kokarin sojojin na kawar da kungiyar Boko Haram.

A cikin wata sanarwa mai cike da kakkausan lafazi da Kakakin rundunar kanal Sani Usman Kuka sheka ya fitar a ranar Alhamis, ya ce rundunar ta gano wasu taruka na sirri da kuma amfani da wasu kungiyoyi da wadannan mutanen ke yi don ganin cewa sojojin ba su cimma wa'adin watanni uku da shugaban kasa ya basu ba.

Rundunar Sojiojin ta ce da alama wadannan mutane na amfana daga aikace-aikacen mayakan Boko Haram don haka ba son ganin an kawo karshensu.