'Yan sanda sun kubutar da Cif Olu Falae

Hakkin mallakar hoto Nigeria Police website
Image caption Shugaban 'yan sanda ne ya jagoranci aikin kubutar da Cif Falae

Rahotanni daga Jihar Ondo sun tabbatar da cewa Cif Olu Falae tsohon sakataren gwamnatin tarayya a Naijeriya ya samu 'yan cin kansa, bayan shafe tsawon kwanaki uku a hannun wadanda su ka yi garkuwa da shi.

Kwamishinan watsa labarai a jihar shi ya tabbatar wa da wakilin BBC da ke a Legas cewar Falae ya koma gida.

Sai dai babu karin haske ko an biyya fansa kafin a ceto shi.

A ranar Litinin ne dai wasu 'yan bindiga suka sace Mr Falae a gonarsa da ke Akure babban birnin jihar Ondo.