'Za a fara samar da wutar lantarki daga iska'

Hakkin mallakar hoto RIA Novosti
Image caption Samun wutar lantarki mai dorewa a Najeriya sai an sabunta tsoffin injina inji shugaban KEDCO

Daya daga cikin kamfanonin samar da wutar lantarki a Najeriya ya ce zai shiga harkar samar da wutar Lantarki ta hasken rana da kuma iska.

Shugaban hukumar samar da wutar lantarki ga jihohin Sokoto da Kebbi da Zamfara da kuma Kaduna KEDCO, shine ya shaida wa BBC hakan a wata hira.

Injiniya Garba Haruna ya ce "dole ne a sabunta naurorin samar da wutar lantarki a Najeriya saboda wadanda ake da su sun tsufa."

Kamfanonin da ke raba wutar lantarki a Najeriya na cewa kafin nasarar da aka samu ta wadatar wuatr ta dore sai an samar da hanyoyin samar da lantarki na daban a maimakon hanyar ruwa watau Hydro Power wacce kasar ta dogara ita.

A baya-bayan nan hasken wutar lantarki ya inganta a kasar, a inda ake samun wutar lantarkin ta sa'o'i masu yawa.