An rusa rundunar sojojin da ke tsaron fadar shugaban Burkina Faso

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Michel Kafando

Gwamnatin Burkina Faso ta rusa rundunar sojojin da ke tsaron fadar shugaban kasa wadan da suka yi garkuwa da ministoci a makon da ya gabata a yayin wani juyin mulkin da bai yi tasiri ba.

An dai dauki matakin ne a wajen wani taro da aka gudanar a ranar larabar da ta wuce bayan da shugaban rikon kwarya na kasar Michel Kafando ya dawo mulki.

An kuma kori ministan da ke kula da al'amuran tsaro tare da kafa wata hukuma wadda za ta yi aiki wajen gano wadan da ke da hannu a juyin mulkin.

Akalla mutane 10 sun mutu a lokacin da ake zanga-zangar nuna kin amincewa da karbar mulki a kasar.

A kwanakin baya ne dai masu tsaron shugaban kasar su ka yi dirar mikiya a wajan wani taron ministoci, inda suka tsare shugaban rikon kwaryar da piraminstan kasar.