An kai hari a ofishin SSS a Lokoja

Wasu 'yan bindiga a Najeriya sun kai hari kan ofishin 'yan sandan farin kaya (wato SSS) da ke Lokoja, babban birnin jihar Kogi.

Kwamishinan 'yan sandan jihar ya ce an yi musayar harbe-harbe na tsawon lokaci yayin artabu da 'yan bindigar.

Ya ce dan sanda daya ya rasa ransa sannan an kuma kashe 'yan bindiga uku.

A baya dai an sha yin yunkurin balle gidan yarin birnin domin sakin 'yan Boko Haram din da ake tsare da su a ciki.

Wannan hari dai na zuwa ne kwanaki kadan bayan wata sanarwa da rundunar 'yan sandan ta jihar Kogi ta bayar na kama wasu mutane 70 wadanda ta kira bata-gari.

Karin bayani