Mutane 20 sun mutu a Afrika ta Tsakiya

Hakkin mallakar hoto
Image caption An dade ana tafka rikici a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya

Rahotanni daga Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya sun ce an kashe kimanin mutane 20 a rikicin da ake yi tsakanin Muslim da Kirista a kasar.

Rikicin baya-bayan nan ya tashi ne bayan kashe wani dan Achaba da aka yi a unguwar Musulmai da ke Bangui, babban birnin kasar.

Kimanin mutane 100 kuma sun jikkata.

Dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya sun yi wa yankunan kawanya saboda yadda rikicin ke yaduwa a unguwannin Musulmai da Kirista.

Wani mazaunin wurin, Malam Abdurahman Goni Abacha, ya shaida wa BBC cewa a yanzu haka Musulmai da dama suna cikin wani masallaci a birnin Bangui don neman mafaka, inda sojojin kasar Burundi ke basu kariya.

An jima ana fama da rikice-rikice tsakanin Musulmai da Kiritsa a jamhuriyar Afrika ta tsakiya, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.