Ana zanga-zanga a Mexico

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dubban masu zanga-zanga a Mexico

Dubban mutane ne su ka bi sahun wata zanga-zanga da akeyi a Mexico domin tunawa da zagayowar ranar da aka sace wasu dalibai 43 lamarin da ya fusata al'ummar kasar baki daya.

Iyayen daliban da su ka bace ne suka jagoranci zanga-zangar inda su ka nuna rashin gamsuwar su da bayanin da gwamnati ta yi na cewa 'yan sanda ne suka mika daliban ga wani gungun masu safarar miyagun kwayoyi in da su kuma suka kashe su.

Masu zanga-zangar sun rike hotunan yaran nasu da su ka bace in da suke bin tituna suna wake-wake na nuna rashin jin dadin su.

Shugaban kasar ta Mexico Enrique Pena Nieto ya yi alkawarin gudanar da sabon bincike a kan wannan lamari.

Kazalika Mr Pena Nieto ya sanar da kirkirar wani kwamiti na musamman da zai duba lamarin.

Daliban su arba'in da uku sun yi batan dabo ne a ranar 24 ga watan Satumbar bara a Iguana.