Za'a kada kuri'ar neman 'yanci a Catalonia na Spain

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ana kada kuri'a a Catalonia

Al'ummar da ke zaune a yankin Catalonia na kasar Spain za su kada kuri'a a yau a wani zabe da zai zamo zakaran gwajin dafi wajen goyon bayan samun 'yancin yankin.

Jam'iyyun adawar yankin sun ce samun nasara a zaben zai ba su damar bayyana 'yancin kai.

Gwamnatin Spain wadda ta ki amincewa da gudanar da zaben raba gardama akan wannan batu, tayi watsi da wannan ikirari da al'ummar yankin Catalonia ke yi.

Ana dai kallon zaben a matsayin daya daga cikin abu mai muhimmanci a tarihin kasar ta Spain.