An kai wa gidan yari hari a Jumhuriyyar tsakiyar Afrika

Hakkin mallakar hoto

Mayakan sa kai na adinin kirista sun kai hari a wani gidan kaso a Bangui, babban birnin Jumhuriyar tsakiyar Afrika, inda suka saki daruruwan fursnoni.

Lamarin ya faru ne lokacin da aka fuskanci tashin hankali tsakanin kiristoci da musulmi da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 30 tun a ranar asabar din da ta wuce.

Mayaka rike da makamai na sintiri a kan tituna tare kuma da dasa shinge.

Dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar dinkin duniya da kuma kasar Faransa su na kokarin dawo da doka da oda.

Shugabar kasar na wucin gadi, Catherine Samba Panza, ta dakatar da ziyarar da ta kai zauren Majalisar dinkin duniya domin ta dawo gida.