An kai wa wayoyin komai da ruwanka hari a China

Masu amfani da wayoyin komai da ruwanka sama da dubu 650,000 a kasar China ba su san an sa su a wata gagarumar satar bayanai ta internet ba.

A harin da aka kai a shafin internet da aka yi wa sata ya samu bukata har sau biliyan hudu da rabi a rana guda.

Hanyar satar ta kunshi wasu talace -talace ne wadanda suke tattare da wasu bayanai da akwai alamar tambaya akansu.

Sai dai watakila masu amfani da wayoyin ba su san da rawar da suka taka ba, lokacinda aka kai harin.

An dai nuna talace talacen ne a cikin wata manhaja mai farin jini sosai a kasar China a cewar kamfanin Cloudflare da ya bankado satar bayanan.

" Watakila an turawa masu amfani da wayoyin talace -talace da ke tattare da bayanai masu alamar tambaya." a cewar Marek Majkwoski wanda ma'aikaci ne a kamfanin Cloudflare.

Sai dai kamfanin Cloudfale bai ambaci sunan shafin internet din da lamarin ya shafa ba.