Yawan Alhazan Nigeria da suka rasu zai haura 54

Turmutsutsun Alhazai a kasar Saudia
Image caption Turmutsutsun Alhazai a kasar Saudia

Alkaluman da ke kara fita na wadanda suka mutu a turmutsutsun da ya faru a kasar Saudia na nuni da yiwuwar na Najeriya su haura 54.

Sarkin Kano kuma shugaban mahajjatan Nigeria na bana, ya yi kira da a sake duban batun zaman Mina musamman ga alhazan Nigeria dake shan matsananciyar wahala yayin zuwa jifa.

Har zuwa yanzu akwai alhazan da dama da ba a gansu ba, kana akwai manyan motocin 14 dauke da gawawwaki da ba a kai ga shigar da su dakunan ajiye gawawwaki ba saboda cunkoso.

Babban sakataren hukumar aikin hajji ta Kano Malam Abba Yakubu ya shaidawa BBC cewa kawo yanzu alhazan Kano tara ne aka tabbatar sun mutu a turmutsutsun, sannan kuma suna ci gaba da bincika asibitoci dan neman wadanda suka bata.

Kasashen Alhazan da suka rasu;

 • Iran: 169
 • Morocco: 87
 • Egypt: 55
 • Nigeria: 54
 • Indonesia: 41
 • India: 35
 • Cameroon: akalla 20
 • Niger: 22
 • Pakistan: 18
 • Ivory Coast: 14 , 77 sun bace
 • Chad: 11
 • Somalia: 8
 • Algeria: 8
 • Senegal: 5
 • Libya: 4
 • Tanzania: 4
 • Kenya: 3
 • Burkina Faso: 1
 • Burundi: 1
 • Netherlands: 1
 • Tunisia: 1
 • Benin: ba a san adadin ba