Shugaban Nijar ya tsige gwamna

Image caption A tsarin dokar Jamhuriyyar Nijar shugaban kasa na da ikon nada gwammna da sauke shi a duk lokacin da ya so

Shugaban Jamhuriyyar Nijar Alhaji Muhamadou Issoufu ya tsige gwamnan jihar Diffa Malam Yakubu Sumana Gawo daga kan mukaminsa ya kuma maye gurbinsa da Janar Abdu Kaza.

Shugaban kasar ya sanar da wannan sauyi ne a yayin wani taro da majalisar ministocin kasar ta yi ranar Asabar.

Shugaban bai bayar da dalilin yin sauyin ba.

Sabon mutumin da aka nada a kan mukamin tsohon soja ne kuma ya rike mukamai daban-daban na siyasa.

Mukamin gwammna a Jamhuriyar Nijar ba zabe ake yi ba kamar yadda ake yi a makwabciyar kasar Najeriya.

Shugaban kasa na da ikon nada gwamna ko ya sauke shi a bisa tsarin dokar kasar.