Shin Sojoji ne ke da iko a Pakistan?

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Rundunar sojin kasar Pakistan tana da karfi sosai a kasar.

Wasu suna bayyana mulkin sojoji a matsayin abin kaico, wasu kuma sun bayyana shi a matsayin hadin gwiwa tsakanin sojoji da 'yan siyasa domin cimma wata kyakkyawar burin ci gaban kasa.

Lamarin ya soma ne daga wani hari da aka kai wata makarantar a garin Peshawar, a ranar 16 ga watan Disambar shekarar 2014, inda 'yan kungiyar Taliban suka hallaka yara maza 132.

Cikin 'yan kwanaki kalilan, gwamnatin kasar ta fito da tsare-tsare 20, da aka sa wa suna 'National Action Plan' domin fuskantar matsalolin 'yan ta'adda da tsagaita munanan kalaman su da kimata da'awar su da kuma toshe hanyoyin samun kudadensu.

Sojojin kuma suka fitar da sanarwar cewa sun kafa kwamiti da ya hada da 'yan siyasa masu fada a ji da manyan jami'an sirri da kuma sojoji.

Sama da mutane 50,000 ne aka tsare wasu kuma aka kama da zargin hannu a ta'addanci.

Wannan yunkuri ya sa an samu sauki sosai a tashe-tashen hankali na ta'addanci, inda manema labarai ma ba su yi kasa gwiwa ba wurin fitowa da aikin da Janar Raheel Sharif ke yi, ta yadda rundunar sojin ta samu goyon bayan 'yan kasa.

Amma duk da cewar an san kisan makarantar Peshawar ce ta kawo wannan sauyi, mutane na da shakkun ko wannan kwamiti na 'National Action Plan' zai kawo wani canji mai dorewa, saboda ko a baya lokacin mulkin Janar Musharraf a shekarar 2007, an kama dubban wanda ake zargi da tayar da kayar baya kuma daga bisani aka sake su.

Tun da gidajen yarin kasar akwai cunkoso, ana kyautata zaton za ta iya sakan wadannan ma.

'Zabbabun hare-hare'

Akwai tabbacin cewar gwamnatin Pakistan ta na zaban kungiyoyin da ta ke kai wa hari.

Ba a taba mayakan da ke zaune a Pakistan, wadanda aka san sun yi yaki da kasar Indiya a baya a kan yankin Kashmir, haka ma kungiyar Taliban ta Afghanistan da kungiyar Haqqani,wacce ake zargi dai hari Kabul.

An samu sabani, a wurin kawar da kai da aka yi wa kungiyar da ke kiran kanta Jama'at ud Dawa, wacce ake zargi da kai hare-hare a Mumbai a shekarar 2006.

'Yan daba

Wasu suna tsoron za a samu 'yan daba cikin mabiya shugaban rundunar sojin Janar Raheel Sharif, saboda duk an mamaye babban birnin Pakistan, Karachi da hotunan sa.

Yayin da 'yan kasar Pakistan da ke da sassaucin ra'ayi ke nuna damuwa a kan wadannan sauye-sauye, sun yi ammana cewa wannan hadin gwiwa na yaki da ta'addanci na bukatar a hadin kan mutane.

Zaman doya da manja

An hana Mr Sharif shigar da wata kara a kan mutumin da ya cire shi a mulki a baya, watau Janar Musharraf, saboda rundunar sojin kasar bata so a ce an kai wani tsohon kusar ta gaban kotu.

Yanzu dai gwamnati da soja na zaman doya da manja ne, kuma duk ana tunanin har yaushe wannan zaman zai kawo karshen.

Fitacciyar mai yaki wurin kare hakkin bil adama a Pakistan, Asma Jahangir ta ce, "Na koyi darasi a baya, na gano sojojinmu ba mulki suke so ba, mulkin mallaka suke so."