'Illolin shan taba ga huhun bil adama'

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

Masana kimiyya a Biritaniya sun yi bayanin dalilan da suka sa huhun wasu masu shan taba yake da lafiya duk da tsawon lokaci da suka shafe suna shan sigarin.

Nazarin da aka yi a kan sama da mutane dubu 50,000, ya nuna cewar sauyin da ake samu a jerin kwayoyin halittar dan adam yana taimakawa ayyukan da huhu yake yi, kuma yana rage tasirin da shan taba yake yi.

Majalisar masana kimiyya ta ce abubuwan da aka gano a nazarin zai iya samar da sababbin magunguna da za su kara lafiyar huhun.

Amma kuma a cewar masana kimiyyar, ba lallai bane shan sigari ya zamanto zabi mafi kyau ba.

Masana kimiyyar sun kara da cewar mafi yawancin masu shan taba, za su kamu da ciwon huhu.

Amma kuma wadanda ba su taba shan tabar ba ma a rayuwarsu, suma za su iya kamuwa da ciwon huhun.

Masu binciken sun yi nazari a kan lafiya da kuma bayanan da ke kunshe a cikin kwayar halittar dan adam a kan ma'aikatan sa kai a cibiyar ajiye binciken lafiyar dan adam da ke Biritaniya.

'Numfashi a Saukake'

Sun duba cutar COPD wadda ke jawowa mutum ya rika numfashi da kyar da tari da kuma yawan kamuwa da cututtuka a kirji.

An yi ammanar mutane sama da miliyan uku suna fama da wannan yanayin a Ingila kuma yana kunshe da cututtuka kamar na cutar kumburi a makogwaro watau 'bronchitis' da kuma cutar huhu wadda ke saka numfashi da kyar watau 'emphysema'.

Da aka kwatanta masu shan sigari da marasa shan sigari, har da wadanda suke dauke da cutar da kuma wadanda ba su da ita, sun gano cewar wasu bangarorin kwayoyin halittar dan adam da ke rage yuwar kamuwa da cutar da ke jawowa mutum ya rika numfashi da kyar ta COPD.

Saboda haka, hadarin kamuwa da cutar COPD ga masu shan taba wadanda suke dauke da kwayoyin halittu masu kyau kadan ne a kan wadanda basu da kwayoyin halittu marasa kyau.

Farfesa Martin Tobin, daya daga cikin wadanda suka yi binciken a jami'ar Leicester, ya ce kamar kwayoyin halittun suna shafar yadda huhun ya ke girma da kuma halayyarsa idan ya kamu da cuta.

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

Amma kuma ya shaidawa BBC cewar "Babu alamun akwai wata hanya tabbatacciya da za ta kare wani daga hayakin taba - huhunsu zai kasance mara lafiya a kan idan da ba su shan sigari ba".

"Muhimmin abin da mutane za su iya yi domin kare lafiyarsu daga cutar COPD da kuma cututtuka wadanda suka shafi shan sigari kamar ciwon daji da kuma ciwon zuciya shi ne su daina shan taba."

'Sabo'

Shan taba na kuma kara hadarin kamuwa da ciwon zuciya da kuma cututtuka dajin wadanda ba a duba su ba wannan binciken.

Masana kimiyya sun kuma gano wasu bagarorin kwayar halittar dan adam wadanda aka fi saninsu a masu shan tabar a kan wadanda basa sha.

Kamar kuma suna sauya yadda kwakwalwa ke yin aiki da kuma yadda mutum zai iya sabo da sigari cikin sauki, duk da dai sai an tabbatar da hakan.

Farfesa Tobin ya ce "nazarin ya ba da wasu bayanai na ban mamaki a kan yadda jikin dan adam ke aiki wanda a da ba mu da ilimin hakan."