'Yan Taliban sun kai hari a Kunduz

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Rundunar 'yan sanda ta ce mutane da dama sun mutu.

Jami'an gwamnatin Afghanistan sun ce daruruwan mayakan kungiyar Taliban sun kai gagarumin hari a birnin Kunduz da ke arewacin kasar.

Sun kai harin ne ta bangarori daban-daban.

Rahotanni na cewa mayakan sun kai hari a kan wani asibiti, lamarin da ake gani shi ne daya daga cikin manyan hare-hare da kungiyar ta kai a birnin.

Kakakin rundunar 'yan sandan yankin ya ce dakarun gwamnati sun yi ta fafata wa da mayakan na Taliban a wurare a kalla hudu.

Ya kara da cewa mutane da dama sun mutu daga bangarorin biyu.

Lardin Kunduz ya sha fama da fuskantar hare-haren 'yan ta'adda tun daga watan Afrilu.