Syria: Putin da Obama sun yi hannun riga

Hakkin mallakar hoto
Image caption Iran da Rasha na goyon bayan shugaba Assad

Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin ya ce wani babban kuskure ne na rashin aiki da shugaban Syria Bashar al-Assad domin murkushe mayakan IS.

A jawabin da ya yi a wajen babban taron Majalisar Dinkin Duniya, Mr Putin ya ce dakarun gwamnatin Syria su ne kadai ke yaki da ta'addanci gaba da gaba, kamar yadda ya fadi.

Ya yi kiran da a hada kai, kamar irin wanda aka yi aka yaki 'yan Nazi a lokacin yakin duniya na biyu.

Ya kuma kare manufofin 'yan aware masu goyan bayan Rasha a gabashin Ukraine, ya kuma soki manufofin NATO na fadada tasirinta.

'Matsayin Amurka'

A jawabinsa da ya yi a wajan babban taron MDD, shugaba Obama ya yi kiran da a samu daidaito a kan Syria.

Ya ce Amurka a shirye ta ke ta yi aiki da kowace kasa cikin har da Rasha da Iran da kuma tattaunawa kan yadda za a kafa gwamnati ta daban ba tare da shugaba Bashar al-Assad ba.

Amma ya kira shugaban Syrian a matsayin wani azzalumi da ke jefa bama-mabai masu guba akan kananan yara.

Daga bisa ni shi ma shugaban kasar Faransa, Francois Hollande ya yi magana mai zafi a kan batun kafa sabuwar gwamnati a Syria.

Ya ce ba za su yi aiki da mai kashe mutane ba.