Diendere ya bukaci dakaru su miƙa wuya

Image caption Janar Diendere ne ya jagoranci juyin mulki

Sojan da ya jagoranci juyin mulki a kasar Burkina Faso a makon da ya gabata, Janar Gilbert Diendere ya bukaci askarawan fadar shugaban kasar watau RSP su ajiye makamansu.

Matakin ya biyo bayan rahotannin da ke cewa ana harbe-harbe a kusa da barikin dakarun da ke lura da fadar shugaban kasar wadanda suka yi juyin mulki.

Tun da rana dakarun sojin suka kewaye barikin da ke Ouagadougou babban birnin kasar, domin tursasa wa sojojin su kwance damara bayan an maido da mulkin farar hula a kasar.

Rahotanni sun ce sojoji 300 na fadar shugaban kasar watau RSP sun mika wuya.

Tuni aka rufe filin saukar jiragen sama na kasar saboda fargabar tashin hankali.

A makon da ya gabata ne, dakarun da ke gadin fadar shugaban kasar suka yi juyin mulki karkashin jagorancin Janar Gilbert Diendere.

Sakamakon matsin lamba daga wurin kasashen duniya, sai dakarun suka maido da Michel Kafando, shugaban gwamnatin rikon kwaryar kasar a kan mulki.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ana ci gaba da zaman dar-dar a Burkina Faso

A shekarar da ta wuce ne aka kifar da gwamnatin Blaise Compaore wanda ya shafe shekaru 27 a kan mulkin Burkina Faso.