Za a dage zaben Afirka ta Tsakiya

Image caption Shugabar kasar Afrika ta Tsakiya, Catherine Samba Panza a taron Majalisar Dinkin Duniya da aka yi a birnin New York.

Shugabar kasar Jamhuriyar Afrika ta tsakiya, Catherine Samba Panza ta ce za a dage zaben kasar saboda matsalolin tsaro.

Shugabar, wadda ta tabbatar wa BBC da hakan a wajen taron Majalisar Dinkin Duniya ke yi a birnin New York, ta kara da cewa babu wanda ya isa ya tursasa mata ta sauka daga kan mulki.

Masu zanga-zanga sun yi kira da ta sauka daga mukamin ta, tunda ba ta yi nasarar kawo saukin tashin hankalin da kasar ke fama da shi ba.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce dubban mutane ne suka rasa muhallansu sakamakon tarzoma a Bangui, babban birnin kasar, a makon jiya.

Miss Samba Panza ta yanke ziyarar da take yi a New York saboda tunkarar matsalar da ke faruwa a kasar, inda a ranar Litinin da daddare ma fursunoni suka balle daga gidan yari.

Kasar ta shiga halin ha'ula'i ne tunda aka hambarar da tsohon shugaban kasar Francois Bozize a shekarar 2013, kuma an shirya gudanar da zabe a watan Oktoba.