China ta hukunta 'yan jarida a kan "labaran karya"

Hakkin mallakar hoto BBC CHINESE
Image caption 'Yan jarida sun ce gwamnatin China na hukunta su ne saboda ba ta so su wallafa labaran da mutane ke son ji.

Hukumomi a kasar China sun ce sun hukunta gidajen watsa labarai 15 da 'yan jarida 17 saboda sun wallafa labaran karya.

Jami'an kasar sun zargi 'yan jaridar da wallafa labaran karya ba tare da tantance su ba.

Kasar ta China dai ta kaddamar da abin da ta kira yaki da masu aikin jarida ba tare da sun tantance labaransu ba.

Sai dai wasu 'yan jaridar kasar sun yi amannar cewa kasar tana musguna musu ne domin tsoron kada su wallafa labaran da ba za su yi mata dadi ba.