Ni zan rike ma'aikatar man fetur — Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaba Muhammadu Buhari

Shugaban Nigeria Muhammadu Buhari, ya tabbatar da cewa yana da aniyyar shi da kansa ya ja ragamar ma'aikatar man fetur ta kasar yayin da yake ci gaba da yaki da karbar hanci da rashawa.

Kawo yanzu dai Shugaba Buhari bai sanar da sunayen ministocinsa ba tun bayan da aka rantsar da shi a watan Mayun wannan shekarar.

A kwanakin baya ne dai shugaban kasar ya sha alwashin bankado makuden kudaden da aka sace a bangaren albarkatun man fetur na kasar, bangaren da ke samar da kashi 70 cikin 100 na kudaden da gwamnatin kasar ke samu.

Nan gaba kadan ne dai ake sa ran shugaba Muhammadu Buhari zai mika sunayen ministocinsa ga Majalisar dattawan kasar domin a tantance su.