Majalisa ta dage zamanta babu sunayen ministoci

Majalisar dattijan Nigeria ta dage zamanta na ranar Laraba amma ba ta yi magana ba a kan batun ko fadar shugaban kasar ta aiko sunayen wadanda za a nada a matsayin ministoci.

Shugaban majalisar, Sanata Abubakar Bukola Saraki shi ne ya sanar da dage zaman majalisar har zuwa ranar shida ga watan Oktoba kafin sanatoci su koma bakin aiki.

Shugaba Buhari ya yi alkawarin ba da sunayen ministocinsa a watan Satumba amma bisa dukkan alamu har yanzu wannan alkwari ya bai cika ba.

Za mu kawo muku karin bayani a nan gaba.