Ana yunkurin kwato Kunduz daga hannun Taliban

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Tuni dai aka kwato ofishin 'yan sandan da 'yan Taliban suka karbe.

Jami'an tsaron Afghanistan na can suna yunkurin kwato birnin Kunduz, kwana daya bayan 'yan kungiyar Taliban sun kwace shi lokacin munana hare-haren da suka kai masa.

Wani wakilin BBC ya ce har yanzu kashi uku cikin hudu na birnin yana hannun 'yan Taliban, ko da ya ke ana samun wasu mutane da ke bijire musu.

Rahotanni na cewa jami'an tsaro sun kwato gidan yari da hedikwatar rundunar 'yan sandan yankin daga hannun Taliban.

Dakarun Amurka da ke Afghanistan sun ce sun kaddamar da hare-hare ta sama a kan birnin.

Ana kallon kwace birnin da 'yan Taliban suka yi a matsayin wata babbar gazawar gwamnatin Shugaba Ashraf Ghani, wanda ya hau kan mulki shekara guda da ta wuce..

Birnin shi ne lardi na farko da 'yan ta'adda suka kwace tun da Amurka ta mamaye kasar a shekarar 2001.