'Yan gudun hijira 500,000 sun shiga Turai

Hakkin mallakar hoto Getty

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta majalisar dinkin duniya ta ce 'yan cirani da 'yan gudun hijirar da suke shiga turai a wannan shekarar sun haura rabin miliyan, yawan da ya nunka wadanda suka shiga nahiyar a shekarar 2014.

Alkaluman da aka fitar na baya-bayan nan sun bayyana cewa sama da mutane 514,000 ne suka yi wannan tafiya ta teku kuma suka rayu.

An kuma jero sunyen kusan mutane 3,000 wadanda suka mutu ko suka bata.

Majalisar dinkin duniya ta ce yawanci wadanda suka isa nahiyar sun fito ne daga yankunan da ake rikice-rikice kuma mafi yawansu daga Syria suke.

Hukumar ba ta san ran wadannan alkaluma za su ragu, yayin da lokacin sanyi ke gabatowa.