Fim kan shirin cin hanci a Ghana ya yi kasuwa

Image caption Dan jaridar Ghana ya shirya fim kan badakalar cin hanci da ta shafi bangaren shari'ar kasar.

An fitar da wani fim a Ghana mai kama da na Hollywood, sai dai shi wannan fim mai tsawon sa'o'i uku an shirya shi ne a kan abubuwa da suka shafi lalata da cin hanci da suka faru a bangaren shari'a na kasar.

A iya cewa wannan fim dai yana nuna kan badakalar cin hanci mafi girma da ya shafi bangaren shari'a a tarihin kasar.

Binciken da dan jarida Anas Aremeyaw ya yi cikin shekaru biyu ya bashi damar tattaro bayanan shaida na tsawon sa'o'i 500 a bidiyo kan lamarin.

Bidiyon ya nuna yadda alkalai da ma'aikatan kotu suke karbar hanci daga masu shigar da kara, har ma da masu neman yin lalata da mata duk domin a yi murda shari'a.

'Kallon fim kyauta'

A yanzu haka ana nuna fim din mai taken 'Ghana in the eyes of God; Epic of Injustice,' a kyauta a birnin Accra.

Mista Anas ya zabi a bayyana fim a bainar jama'a saboda barazanar da ake yi wa kafofin yada labarai, da cewa za a kai su kotu idan sun nuna shi.

Amma ya ce yana bukatar mutane da dama su kalli irin aikin da ya yi, ya kuma ce "mutane ne suke bukatar adalci a shari'a ya kuma kamata su san yadda shari'a take a kasar nan."

Waye Anas Aremaeyaw?

Image caption Anas ba ya taba fita ba tare da ya sauya kama ba.

Anas Aremeyaw ya fita daban da sauran mutane, inda baya taba fitowa cikin jama'a ba tare da ya badda kama ba.

Masoyansa na masa kallon wani hamshakin gwarzo cikin ma'aikatan jarida, inda ya shafa shekaru 15 yana badda kama wurin neman labarai a sirrance, har da shiga irin ta mata, da jan baki da takalmi mai tsini.

'Adawa da kallon fim'

Image caption Yadda mutane ke cika sinima don kallon fim din.

Ba abun mamaki bane yadda Alkalan ba sa so a nuna fim din, dalilin haka ma ya sa aka hana wasu gidajen sinima nuna fim din.

Hakan dai bai hana kallon ba.

Fim din dai an shirya shi ne a wani dakin sirri da Mista Anas ke hada fina-finai.

Ya nuna yadda Alkalai ke karbar hanci daga wajen masu shigar da kara, wani lokacin a cikin mota, wani sa'in kuma a ofis ko a gida.

An kuma nuna yadda ake bayar da kudi da yadda ake lalata da wasu.

Wakilin BBC ya ce lokacin da ya je daya daga wajen da ake nuna fim din 'yan kallo su kan barke da sowa musamman a duk sanda aka nuna wajenda ake lalatar.

A wasu lokutan kuma sai ka ji an yi tsit wanda hakan ke nuna yadda mutane suke tattauna lamarin tsakaninsu da zuciyarsu.