Alhazan Mali da Ethiopia 62 sun rasu

Image caption Hukumomin Saudiyya sun ce za su gudanar da bincike kan lamarin

Hukumomi a kasashen Mali da Ethiopia sun bayyana cewa alhazansu 62 ne suka rasu sakamakon turmutsitsin da aka samu a kusa da wurin jifan shaidan a Saudiyya.

Gwamnatin Mali ta ce mahajjata 50 ne 'yan kasarta suka rasu sakamakon hadarin da ya auku a makon da ya gabata.

Haka kuma 'yan kasar Mali 40 ne suka jikkata sai kuma wasu 100 da har yanzu ba a ji duriyarsu ba.

Ita kuma majalisar koli ta addinnin Musulunci a kasar Ethiopia ta ce alhazanta 12 ne suka rasu sannan wasu kuma 26 suka jikkata sakamakon turmutsitsin.

Tuni dai hukumar kula da aikin hajji ta Nigeria ta tabbatar da rasuwar alhazai 64 a yayin da mutane 71 suka samu raunuka sai kuma alhazai 244 da ba a san inda suke ba.

Rahotanni dai sun nuna cewar yawan alhazan da suka rasu a hadarin da ya auku ranar Alhamis ya haura mutane 1,000.

Alkaluman da hukumomin Saudiyya suka fara fitarwa dai na cewa sama da mutane 700 ne suka mutu.