An kashe dan Indiya saboda cin naman shanu

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Gwamnatin Indiya ma ta tsaurara dokokin haramta cin naman shanu

A ranar Laraba ne wasu gungun mutane suka yi wa wani Musulmi duka har suka kashe shi saboda zargin shi da iyalansa suna cin naman shanu.

An haramta cin naman shanu a yawancin jihohin Indiya saboda masu addinin Hindu wadanda sune mafi yawa a kasar sun mayar da shanu abin bautarsu.

Gungun mutanen sun shiga har cikin gidan Mohammad Akhlaq da ke jihar Uttar Pradesh a arewacin kasar, inda sukai masa duka har ya mutu suka kuma ji wa dansa rauni.

Tuni 'Yan sanda suka kama mutane shida da ake zargin suna daga cikin mutanen da suka aikata wannan lamari.

A baya-bayan nan ma gwamnatin Indiya ta tsaurara dokar haramta yankawa da sayarwa da kuma cin naman shanu.indiya