Rasha ta soma luguden wuta a Syria

Hakkin mallakar hoto
Image caption Jiragen yakin Syria

Rasha ta ce jiragen yakinta sun fara kai hare-hare ta sama a cikin Syria.

Ma'aikatar tsaron kasar ta ce jiragen sun jefa bama-bamai a wasu wuraren kungiyar IS, amma dai jami'an Amurka sun ce kamar wajen ba a hannun kungiyar ya ke ba.

Wannan dai ya faru ne sa'o'i bayan da majalisar dokokin Rashar ta amince da bukatar da shugaba Putin ya mika mata na tura sojoji kasar zuwa waje.

Mr Putin ya ce Rasha za ta yi amfani da karfi ne ta sama kawai ban da kasa.

Kakakin shugaba Putin, Sergei Ivanov, ya ce "Aikin sojojin shi ne tallafawa gwamnatin Syria ta sama kawai domin yakar kungiyar IS."

Gwamnatin Syria ta ce shigar sojojin Rashar ya biyo bayan neman taimakon da shugaba Bashar al- Assad ya yi ne.