Majalisa na jiran sunayen Ministoci

Image caption Tuni 'yan Najeriya suka kagu a fitar da sunayen ministoci

Majalisar Dattawan Najeriya ta fara zamanta na ranar Laraba ba tare da sanarawar karbar sunayen ministoci ba.

Shugaban Majalisar, Sanata Bukola Saraki, ya karanto abubuwan da za a duba yayin zaman, amma bai ambato sunayen ministoci ba.

Hakan ne ya sa Shugaban Marasa Rinjaye, Godswill Akpabio, ya yi hannunka-mai-sanda ga shugaban majalisar.

Sai dai kuma Mataimakin Shugaban Masu Rinjyae Bala Ibn Na'allah ya shaida masa cewa 30 ga watan Satumba ba za ta wuce ba har sai karfe 12 na dare.

Tuni 'yan Najeriya suka kagu su ji sunayen wadanda za a nada ministocin kasar.

A zaman da majalisar ta yi ranar Talata, Mista Saraki ya sanar da cewa a ranar Laraba za su fara duba jerin sunayen ministocin da za a gabatar musu, sai dai bai ce komai ba a kan ko sun sami wani bayani daga shugaban kasa.