Buhari ya aika sunayen ministoci majalisa

Hakkin mallakar hoto Nigeria Senate
Image caption Lokacin mika sakon shugaba Buhari

Shugaban majalisar dattijan Nigeria ya ce shugaban kasar Muhammadu Buhari ya aika ma sa jerin sunayen mutanen da yake son su zama ministoci.

Sanata Abubakar Bukola Saraki ya rubuta a shafinsa na Twitter cewa ya samu sunayen amma kuma bai bayyana wadanda ke cikin jerin ba.

Babban ma'aikaci a fadar shugaban kasa, Alhaji Abba Kyari da mataimakin shugaban kasa a kan harkokin majalisar dattijai, Sanata Ita Enang.

Dama dai Shugaba Buhari ya bayyana cewar shi ne zai jagoranci ma'aikatar harkokin man fetur.