Na'urorin kiwon lafiya na fuskantar kutse

Hakkin mallakar hoto SPL
Image caption Na'urorin kiwon lafiya dubu 68,000 ke fuskantar barazanar kutse.

Dubban na'urorin da ake amfani da su wajen kula da lafiya da suka hada da naurar binciken cuttuttukan a jikin dan Adam wato MRI na fuskantar barazana daga masu kutse a shafukan Internet a cewar wasu masu bincike.

Masu binciken sun ce kimanin na'urorin kiwon lafiya dubu 68,000 da wasu kamfanonin Amurka ke samar wa ke fuskantar wannan barazana.

Masu bincike kan sha'anin tsaro da suka hada da Scott Erven da Mark Collao ne suka gabatar da sakamakon binciken su a wani taro da aka gudanar kan matsalar kutse a Internet a Derbycon.

Sun kuma bayyana cewa sun kirkiro wasu kayayyakin kiwon lafiya na bogi wadanda suka ja hankalin dubban masu kutse a Internet.